’Yan bindiga sun sace Basarake a Filato

’Yan bindiga sun sace Basarake a Filato

’Yan bindiga sun sace Basarake a Filato

‘Yan Bindiga

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace Joshua Makut, wani basaraken gargajiya a Jihar Filato.

Joshua dai shi ne basaraken gundumar Mushere da ke Karamar Hukumar Bokkos a Jihar.

Gwamnan Jihar ta Filato, Caleb Mutfwang ne ya tabbatar da sace basaraken ranar Litinin.

Gwamnan na jawabi ne yayin wani biki na musamman da aka shirya domin Ranar Dimokuradiyya ta bana a Jos, babban birnin Jihar.

Ya ce an sace basaraken ne a fadarsa da daren Lahadi, kuma har yanzu babu cikakken bayani kan inda maharan duka kai shi.

An kai hari Fadar Shugaban Ƙasar Chadi

Ambaliyar Ruwa: Mutum 24 sun rasu, an tallafa wa magidanta 1,000 a Bauchi

’Yan sanda sun kama ’yan damfara 5 a Yobe

Nan ba da jimawa za a ƙara kuɗin kiran waya da data — Gwamnati