’Yan bindiga sun sace basarake a Jihar Filato

An sace shi ne a cikin gidansa da safiyar ranar Lahadi.

’Yan bindiga sun sace basarake a Jihar Filato

’Yan bindiga

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken garin Gindiri da ke Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.

Aminiya ta gano cewa maharan dai sun sace basaraken be a cikin gidansa bayan sun yi harbe-harbe da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Manjo Ishaku Takwa, Kakakin rundunar tsaro ta  ‘Operation Safe Haven’ (OPSH), wacce ke aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin, shi ne ya tabbatar da hakan.

Sai dai ya ce tuni rundunar ta baza dakarunta a yankin kuma suna nan suna bin diddigin masu garkuwar.

Ya sha alwashin cewa za su kubutar da shi nan ba da jimawa ba daga hannun wadanda suka sace shin.