’Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 13 a Abuja
A cikin dare ’yan bindigar suka kutsa kauyen Chida da ke Karamar Hukumar Kwali suka sacw mutanen.
’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake tare da wasu mutum 13 a Yankin Babban Birnin Tarayya.
A cikin dare ne ’yan bindigar suka kutsa cikin kauyen Chida da ke Karamar Hukumar Kwali suka yi awon gaba da mutanen.
- An caka wa limami wuka yana tsaka da jan Sallah a Amurka
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da ’Yan Najeriya Ke Gudun Kayayyakin Da Aka Yi A Kasar
Wani dan unguwar mai suna Ishaya Musa, ya bayyana cewa maharan sun kuma harbi wani matashi mai shekara 18 da ya yi kokarin tserewa.
Ishaya Musa ya bayyana cewa a daren Juma’a maharan suka shigo suna harbi da bindigogi kirar AK-47 suka je kai-tsaye zuwa fadar basaraken suka dauke shi, kafin daga bisani su dauke sauran mutanen.
A cewar Ishaya, “Saboda firgita da karar harbe-harben, yaron ya yi kokarin tserewa, shi ne suka harbe shi a kafa, amma an kai shi asibiti.”
Sauran mutanen da aka dauke, suna kwakkwance ne a waje ne saboda tsananin zafi, lokacin da aka kai harin.
Ya ce a ranar Asabar da yamma jagoran ’yan bindigar ya kira iyalan wadanda aka sacen ya yi magana da su.
Kauyen Chida na da nisan kilomita uku daga Bukpe, kauyen da a bara ’yan bindiga suka sace basarakensa, Alhaji Hussaini Shamdozhi.
Bana kuma aka yi garkuwa da matarsa da ’ya’yansa uku a watan Fabrairu.