’Yan bindiga sun sace dalibai a Jami’ar Jihar Kogi

Maharan sun ritsa dalibai da ke cikin aji suna shirye-shiryen zana jarbawa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi (CUSTECH)

’Yan bindiga sun sace dalibai a Jami’ar Jihar Kogi

’Yan bindiga sun kai hari inda suka sace dalibai da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi (CUSTECH).

A daren Alhamis ne ’yan bindigar suka kutsa harabar jami’ar da ke yankin Osara, inda suka dauke dalibai da kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Wani dalibin jami’ar wanda ya tsallake rijiya da baya, mai suna John, ya shaida mana cewa “Misalin karfe 9 na dare muka fara jin karar harbi a lokacin da muke cikin dakunan karatu saboda muna shirye-shiryen jarabawa.

“Wasu sunnmu sun tsere, amma na san an kama wasu dalibai”, in ji wani dalibin jami’ar mai suna John.

Rahotanni daga jami’ar sun ce ’yan banga da ke yankin sun kai dauki, amma maharan sun fi su karfin makamai.

Zuwa wannan lokaci dai babu cikakken bayani saboda mahukunta sun ki cewa komai a kai,  sai nan gaba.

Mun tuntubi kakakin ’yan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, amma har muka kammala rubuta wannan labarin ba mu ji daga gare shi ba.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa