’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Jami’ar ba fitar da wata sanarwa kan faruwar lamarin ba.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

’Yan bindiga sun sace Farfesa John Ebeh Malami a Sashen Falsafa na Jami’ar Prince Abubakar Audu (PAAU), da ke Anyigba, a Jihar Kogi.

Maharan sun nemi a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 10.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Alhamis, a yankin Agbeji, na garin Anyigba da ke Ƙaramar Hukumar Dekina.

Maharan sun kai farmaki gidan Farfesan, inda suka dinga harbe-harbe don razanar da jama’a kafin su tafi da shi.

Wani maƙwabcinsa mai suna Akpai ya ce: “Sun kai harin cikin sauri, kamar a fim.

“Da farko, mun ga wata mota na binsa, mun ɗauka wani abokinsa ne. Sai kawai muka fara jin harbe-harbe a kusa da ƙofar gidansa.”

Wani daga cikin iyalansa ya bayyana cewa Farfesa Ebeh na kan hanyarsa ta dawowa gida lokacin da lamarin ya faru.

“Ya kusa isa ƙofar gidansa a Agbeji, sai kawai wata mota ta tsayar da shi. Daga nan wasu mutane ɗauke da bindigogi, wasu sanye da takunkumi, suka fito daga mota, suka dinga harbe-harbe suka kuma tafi da shi.

“A daren ranar Juma’a suka kira iyalinsa suna neman a biya su Naira miliyan 10.”

Har yanzu jami’ar ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba, amma wani abokin aikinsa ya bayyana damuwarsa kan faruwar lamarin.

“Abin ya girgiza mu sosai. Na ziyarci iyalansa don jajanta musu,” in ji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi, SP Williams Aya, bai amsa zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba.

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra

Abba ya buƙaci sabbin Kwamishinoni su cika muradun Kanawa

Zulum ya sanya hannu kan kasafin 2025 na N615.8bn