’Yan bindiga sun sace fasto da iyalinsa, sun nemi N75m a matsayin kuɗin fansa
An sace fasto ɗin da iyalansa yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Ikaram.
’Yan bindiga sun sace wani fasto, Rabaran Canon Olowolagba, matarsa da ’ya’yansa biyu a Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa Maso Gabas, a Jihar Ondo.
Sun sace shi tare da matarsa da ’ya’yansa biyu a ranar Lahadi da ta gabata.
- Tinubu ya damu game da harin Sakkwato – Minista
- Abba ya tarbi ɗaliban Kano 150 da suka kammala digiri na biyu a Indiya
Rabaran Olowolagba, wanda ke aiki a cocin Akoko Anglican Diocese, yana tare da iyalinsa lokacin da ’yan bindigar suka tare su.
Ɗaya daga cikin ’ya’yan nasa da aka sace, Goodness, ɗaliba ce a ajin farko na Jami’ar Adekunle Ajasin (AAUA), wadda ta dawo gida domin yin hutun Kirsimeti.
Fasto ɗin cocin Anglican Diocese, Babajide Bada ne, ya tabbatar da lamarin a ranar Asabar a Akure.
Ya ce fasto ɗin da iyalansa na tafiya daga Ipesi ta Isua Akoko lokacin da ’yan bindiga suka tare motarsu suka kai su daji.
“Lamarin ya faru ne ranar Lahadin da ta gabata tsakanin ƙarfe 4 na yamma zuwa 5:30 na yamma,” in ji Bishop.
“Suna kan hanyarsu ta zuwa Ikaram lokacin da aka sace su. Waɗanda aka sace sun haɗa da Rabaran Olowolagba, matarsa, ‘yarsu ‘yar shekara 16, Goodness, da wata yarinya ‘yae shekara tara mai suna Idowu.”
’Yan bindigar sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 75 kafin su sake su.
An kai rahoton lamarin ga jami’an tsaron Amotekun, mafarauta, da kuma ’yan sandan Ikare da Isua Akoko.
“Amotekun da mafarauta sun fara bincike a daji don ceto waɗanda aka sace,” in ji shi.
Sheikh Basiru Aminu, Shugaban Majalisar Koli na Harkokin Addinin Musulunci a Akoko Arewa Maso Gabas, ya yi kira ga shugabannin addini da al’ummar yankin da su yi addu’a don kuɓutar waɗanda aka sace.
Shugaban jami’an tsaron Amotekun, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da sace su, ya kuma bayyana cewa suna aiki tare da sauran hukumomin tsaro don ganin an sako waɗanda aka sace.
Sai dai kakakin rundunar ’yan sanda Jihar Ondo, Funmi Odunlami, ta ce ba a kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda ba.