’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina

Maharan sun sace gwarzon ne tare da mahaifinsa da wasu ‘yan uwansa.

’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina

’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya samu a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi.

Wani jami’in gwamnati a Faskari, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace su.

“Malam Rabe da ’ya’yansa biyar, ciki har da Abdulsalam, wanda aka sace su a Bangori a kan titin Yankara. Har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.”

Abdulsalam, wanda ɗalibi ne a sashen likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ya samu matsayi na farko a gasar a ɓangaren maza bayan ya haddace Alƙur’ani.

Har yanzu ’yan sanda a Katsina ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.