’Yan bindiga sun sace hadimin Gwamnan Kuros Riba
Lamarin dai ya faru ne da safiyar ranar Talata a birnin Kalaba na Jihar.
Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade
Akalla wasu ’yan bindiga da yawansu ya kai kusan 10 sun sace Mai ba Gwamnan Jihar Kuros Riba Shawara a kan Bunkasa Noman Koko, Mista Oscar Ofuka.
Lamarin dai ya faru ne da safiyar ranar Talata a harabar Kafar Watsa Labarai ta Jihar ta Kuros Riba (CRBC) inda hadimin ya je domin halartar bikin kaddamar da wani shiri kan noman Kokon wanda Mataimakin Gwamnan Jihar, Farfesa Ivara Esu ya shirya.
A cewar wani dan jarida da ke aiki da kafar ta CRBC, Mista Sunny Inah wanda a kan idonsa lamarin ya faru, da farko wasu mutane biyu ne sanye da kakin ’yan sanda suka yi yunkurin yin awon gaba da shi a harabar CRBC din.
Ya ce, “Amma lokacin da ya yi yunkurin tirjiya, sai na ga wasu wadanda yawansu ya kai kusan 10 dauke da bindigogi suka tura shi ta karfin tsiya sai a ya shiga cikin wata motarsu ja kirar Range Rover.
“Sai da ma suka yi barazanar harbin wasu daga cikinmu da suka zo domin taimaka masa, yayin da shi kuma shugaban tashar, Maurice Mainok da wata ma’aikaciya, Esther Ofem aka ture su,” inji Mista Sunny.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar, Mista Kayode Sikiru ya ce tuni suka baza jami’ansa domin kokarin ceto hadimin Gwamnan.
Watanni biyu da suka gabata dai Mista Ofuka ya kira wani taron ’yan jarida a Kalaba inda ya yi zargin cewa wani tsohon Mataimakain Sufeta Janar na ’yan sanda na barazana ga rayuwarsa, inda ya ce ya sha turowa a kai masa hari.
A lokacin dai, ya ce tsohon dan sandan na zarginsa da kin ba da wasu filayen bishiyar Koko ga wasu masu ido da kwalli a Jihar.