’Yan bindiga sun sace hakimi da limami a Zamfara
Maharan sun karbi dubu 500 sun kuma ki sakin hakimin da limamin da suka sace.
’Yan bindiga sun yi awon gaba da hakimin Rakyabu Rakyabu, Magaji Sa’idu da kuma babban limamin kauyen, Malam Abdullahi, da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata lokacin da ’yan ta’addan suka kai hari kauyen, amma har yanzu ‘yan sandan ba su tabbatar ba.
- ’Yan Najeriya 260,000 sun nemi yin hijira daga kasar a 2023 —IOM
- ’Yan bindiga na neman N16m da 4 babur kan mutane 11 a Kaduna
Kakakin ’yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ya shaida wa Aminiya cewa, “Ba ni da labarin faruwar lamarin, na dawo daga tafiya ne, amma zan tuntubi DPO na Tsafe.”
Amma wani mazaunin yankin ya ce maharan sun bukaci al’ummar kauyen su ba su Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa.
A cewarsa, al’ummar kauyen dubu 500 suka iya hadawa domin biyan fansar hakimin da limamin, wanda maharan suka karba amma suka ki sako shi.
“Sun ce dole ne mu cika ragowar Naira miliyan 4.5, ba su saki wadanda suka sace ba har yanzu.
“Muna neman tallafi daga hukumomin da abin ya shafa don taimaka mana wajen ganin wadanda aka sace sun kubuta, mun yi iya kokarinmu tun makon da ya gabata.”
‘Yan bindiga sun dade suna ta’addanci a wasu jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda suke kai hare-hare tare da sace mutane domin neman kudin fansa.
A yankin Arewa Maso Gabas kuwa an fatattaki mayakan Boko Haram da suka jima suna kashe mutane.
Fiye da mutane 40,000 ne aka kashe tare da raba miliyan biyu da muhallansu tun daga 2009 zuwa yanzu.