’Yan bindiga sun sace hakimi da manoma 2 a Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewar an sace hakimin ne lokacin da yake dawowa daga gona.

’Yan bindiga sun sace hakimi da manoma 2 a Kaduna

’Yan Bindiga sun yi garkuwa da Hakimin Tunburku, Malam Ashiru Sherehu da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewar, maharan sun yi awon gaba da Sherehu a kan hanyarsa ta dawowa daga gona a ranar Asabar.

’Yan bindiga sun addabi yankin da ke gundumar Fatika a ‘yan kwanakin nan da hare-hare.

A cewar wani mazaunin yankin, Ahmadu, manoma ba sa iya zuwa gonakinsu da ke da nisan kilomita kaɗan daga garin saboda tsoron kada a kashe su ko kuma a sace su.

Wani basaraken gargajiya a yankin kuma Sarkin Fadan Galadimawa, Husseini Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi garkuwa da hakimin ƙauyen da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Asabar.

“Yana dawowa daga gonarsa da ke Tunburku sai ‘yan bindigar suka tare shi suka tafi da shi. Har yanzu ba mu ji daga gare su ba; kuma ba su tuntuɓe mu ba,” in ji shi.

A cewar Hussaini, an kuma sace wasu manoma biyu a yankin Sabon Layi da ke gundumar Kidandan a lokacin da suke aiki a gonakinsu a ranar Lahadi da rana.

Ya bayyana cewar mutanen ƙauyen da lamarin ya faru a gabansu sun kasa yin komai saboda ’yan bindigar na ɗauke da makamai.

Umar, ya koka kan yadda ’yan bindiga ke yi wa manoma ɗauki ɗai-ɗai a yankin.

Amma, ya yaba da ƙoƙarin sojojin da aka tura yankin, sai dai ya roƙi gwamnati da ta aike da ƙarin jami’an tsaro masu yawa saboda yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a yankin.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ba ta ce komai kan faruwar lamarin ba.

Jin ta bakin kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan, ya ci tura domin ba ya amsa kiran waya.