’Yan bindiga sun sace hakimi da wasu mutum biyu a Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun sace Hakimin Kujama a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, Steven Ibrahim tare da wasu mutum biyu

’Yan bindiga sun sace hakimi da wasu mutum biyu a Kaduna

Masu garkuwa da mutane

Wasu ’yan bindiga sun sace Hakimin Kujama a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, Steven Ibrahim tare da wasu mutum biyu.

Lamarin ya farune da karfe 7 na yammancin ranar Lahadin nan da ta wuce a lokacin da ya fito daga wani otel da ke a bayan makarantar Bethel da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachia.

Wani jami’in JTF wanda ba ya son a ambaci sunansa ne ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce mazauna wani kauye da ake kira Anguwar Ayaba sun ga lokacin da aka wuce da su a kan barbura.

Shi ma Ardon Ardodi na Chikun, Ibrahim Saleh ya tabbatar wa da Aminiya hakan inda ya yi fatan Allah Ya kawo karshen masifar sace mutane a yankin.

Rundunar ’Yan Sandan jihar har ya zuwa lokacin aika wa da labarin ba ta ce komai ba, kuma shi kakakinta, ASP Mansir Hassan bai amsa rubutaccen sakon da aka aika masa ba, sannan wayarsa ba ta shiga ba.

Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa

Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno 

’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci

Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata