’Yan bindiga sun sace Jakadan Jordan a Libya

Wasu ’yan bindiga a kasar Libya sun sace Jakadan Jordan Fawaz al-Itan a Libyar, bayan sun bude wa motarsa wuta a babban birnin kasar Tripoli ranar Talata.Garkuwa da mutane na ci gaba da karuwa a kasar, wanda hakan ke nuna halin rashin tabbas da kasar ta fada tun bayan hambarar da gwamnatin Marigayi Muammar Gaddafi […]

’Yan bindiga sun sace Jakadan Jordan a Libya
’Yan bindiga sun sace Jakadan Jordan a Libya

Wasu ’yan bindiga a kasar Libya sun sace Jakadan Jordan Fawaz al-Itan a Libyar, bayan sun bude wa motarsa wuta a babban birnin kasar Tripoli ranar Talata.
Garkuwa da mutane na ci gaba da karuwa a kasar, wanda hakan ke nuna halin rashin tabbas da kasar ta fada tun bayan hambarar da gwamnatin Marigayi Muammar Gaddafi a shekarar 2011.
Gwamnatin kasar dai na kokarin karbe iko daga hannun kungiyoyin da ke dauke da makamai da kuma kungiyoyin kabilu da suka jagoranci kawo karshen mulkin fiye shekara 40 na Kanar Gaddafi.
Wani jami’in tsaro da ke jagorantar binciken gano jakadan, Essam Baitelmel ya bayyana cewa wanda suka sace jakadan sun bukaci kasar Jordan da ta saki wani dan Libya da ake tuhuma da kitsa wani hari cikin shekarar 2007 a filin jirgin saman kasar ta Jordan, kafin su sallami Mista Fawaz. Sun dai bayyana bukatar tasu ce ta waya a lokacin da yake magana da su ta waya, inda kuma suka ce jakadan na cikin koshin lafiya.
Amma Ministan Harkokin Wajen Libya ya ce ba zai iya tabbatar da abubuwan da masu garkuwa da jakadan suka bukata ba. Kodayake Firaministan Jordan Abdullah Ensour ya yi kira ga hukumonin Libya da su yi duk abin da ya dace don ganin sun kubutar da jakadan. kanwar jakadan Khawala al-Itan ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press cewa tun da dadewa yayanta ke fuskantar barazanar sace shi daga maharan.   
Idan ba a manta ba, a watan Janairun da ya wuce wasu mahara sun tsare wasu mutane shida ’yan kasar Masar bayan cafke wani kwamandansu da kasar Masar ta yi.