’Yan bindiga sun sace Kansila da wasu mutum 2 a Kaduna

An sace su ne a Karamar Hukumar Soba

’Yan bindiga sun sace Kansila da wasu mutum 2 a Kaduna

‘Yan Bindiga

Wasu da ake zargin ’yan fashin daji ne sun sace Kansilan gundumar Garu da ke Karamar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna, Alhaji Sabitu Ahmad, da wasu mutum biyu.

Bayanai sun nuna cewa ’yan bindigar sun yi dirar mikiya ne a yankin Anguwar Mai Taro da ke a Karamar Hukumar, inda Kansilan ke zaune suka dauke shi da wata mata a unguwar a ranar 19 ga watan Agustan da muke ciki.

Kazalika, an sace wani mutum daya a unguwar Dankande a ranar 18 ga watan Agusta, duk a Karamar Hukumar ta Soba.

Lawal Sani, wani matashi a yankin ya bayyana wa Aminiya cewa Kansilan da aka sace kuma shi ne kakakin Kansaloli na Karamar Hukumar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Mohammed Jalige, bai amsa wayarsa ba da kuma sakon kar-ta-kwanan da wakilinmu ya aike masa.

Shi kuwa mai magana da yawun Gwamnar Jihar, Mohammmed Lawan Shehu da aka tuntube shi cewa ya yi har yanzu ba a sanar da shi a hukumance ba.

Zaɓen Edo: An fara ƙirga ƙuri’u

Zaɓen Edo: INEC ta tsawaita kaɗa ƙuri’a a wasu yankuna

’Yan sanda sun kama mai yi wa ’yan bindiga safarar makamai a Kaduna

Gwamnan Kano ya raba wa makarantu kujeru da tebura 73,000