’Yan bindiga sun sace marasa lafiya da ma’aikatan jinya a Kaduna

Mazauna yankin sun ce ba su san adadin marasa lafiyar da maharan suka sace ba.

’Yan bindiga sun sace marasa lafiya da ma’aikatan jinya a Kaduna

Wasu gungun ’yan bindiga sun kai hari wani asibiti da ke ƙauyen Kuyallo a ƙaramar hukumar Birnin-Gwari a Jihar Kaduna, inda suka sace ma’aikatan jinya mata guda biyu da wasu marasa lafiya da ba a san adadinsu ba.

Shugaban ƙungiyar sa-kai ta yankin, Musa Alhassan, ya ce da farko ’yan bindigar sun nufi makarantar sakandare ta gwamnati da ke yankin, da misalin ƙarfe 9 na safiyar ranar Litinin.

Ya ce bayan da suka iske babu kowa a makarantar, sai suka nufi asibitin.

“’Yan bindigar sun zo makarantar suna tambayar ina ɗalibai, amma da suka ga babu kowa, sai suka nufi asibitin inda suka sace mutane,” in ji Alhassan.

Ya bayyana cewa ’yan bindigar da farko, sun niyyar sace ɗalibai, amma sai suka ɓige da sun yi awon gaba da ma’aikatan jinya mata guda biyu tare da wasu marasa lafiya.

Ya ce lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba.

“Har yanzu ba a san adadin marasa lafiyar da suka sace ba,” a cewarsa.

Wani ganau ya ce, “’Yan bindigar sun shiga asibitin ɗauke da bindigu da adduna. Ta ƙarfin tsiya suka fara ɗauko mutane daga asibitin, kuma ba mu iya yin komai don hana su ba.”

Wannan harin na daga cikin jerin hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Jihar Kaduna, abin da ke ƙara jaddada bukatar inganta matakan tsaro don kare al’umma da cibiyoyin lafiya.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Kazalika, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar kan lamarin.