’Yan bindiga sun sace manajar banki a Bayelsa
An sace ta ne a kan hanyarta ta zuwa ofis
Wasu ’yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace manajar bankin Sterling, Nneka Enuka Ugonochie, a Jihar Bayelsa.
Aminiya ta gano cewa lamarin ya faru ne ranar Juma’a, a kusa da titin Sani Abacha da ke Yenagoa, babban birnin Jihar.
- Gwamnan Kano ya nada ‘dansa’ shugabancin wata hukumar gwamnati
- Mahara sun sace basarake da matarsa a Kogi
Lamarin dai ya zo wa mazauna yankin da yawa da ba-zata, kasancewar akwai shingen binciken ababen hawa masu yawa.
Wasu majiyoyin daga jami’an tsaro sun ce an sha ba manajar shawara da ta bar yankin saboda kusancinsa da inda aka kama wasu kasurguman masu garkuwa, John Ewa da John Lyon da kuma Emmanuel Agase.
Mazauna yankin da dama dai sun shaida wa Aminiya cewa ana zargin cewa ragowar yaran John Lyon din ne wadanda suka gudu lokacin da aka kama maigidan nasu ne suka sace matar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Romokere Ibani, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce maharan a cikin kakin sojoji ne suka sace ta lokacin da take tuki a kan hanyarta ta zuwa ofis.