’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano
Wasu daga cikin matan da aka sace sun tsere bayan harin ’yan bindigar a daren Lahadi, a yankin Ƙaramar Hukumar Shanono
’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano a daren Lahadi, inda suka yi garkuwa mata biyar ciki har da masu shayarwa.
Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen ’Yan Kwada da ke cikin yankin Faruruwa a Ƙaramar Hukumar Shanono da ke Shiyyar Kano ta Arewa.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa dandazon maharan sun yi dirar mikiya a garin ne ɗauke da muggan makamai, suna harbe-harbe tare da shiga gidaje suna yin awon gaba da mutane.
“Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska suna karya ƙofofi. Sun tafi da mata biyar, ciki har da masu shayarwa,” in ji majiyar.
- Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shi
- Mahaifiyar Minista Balarabe Lawal Abas ta rasu
Sai dai ya ce biyu daga cikin matan da aka sace sun tsere sun dawo, yayin da ragowar ukun ke hannun ’yan bindigar.
Harin na daren Lahadi na zuwa ne bayan mako guda da sojoji suka hallaka ’yan bindiga kimanin 19 a yankin.
Mutanen Faruruwa da sauran ƙauyuka da ke kan iyakar Kano da Katsina na cikin fargaba sakamakon hare-haren ’yan bindiga da ke faruwa lokaci zuwa lokaci.
Rahotanni sun ce tsananin rashin tsaro ya sa yawancin ƙauyuka a yankin sun zama kufai, inda jama’a suke tserewa zuwa garin Faruruwa ko kuma birane don tsira da rayukansu.