’Yan bindiga sun sace mata 50 a Zamfara 

’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Kakin Dawa da ke yankin Gidan Goga, inda suka yi awon gaba da mata sama da 50 a Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.

’Yan bindiga sun sace mata 50 a Zamfara 

Dajin da Sheikh Gumi ya yi wa ‘yan bindiga da’awa a Jihar Neja, daya daga jihohin da ke fama da matsalar tsaro. (Tsohon hoto).

’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Kakin Dawa da ke yankin Gidan Goga, inda suka yi awon gaba da mata sama da 50 a Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce maharan sun sace mata da yara sama da 50 a lokacin da suka kai harin.

Wani mazaunin ƙauyen ya bayyana cewa ’yan bindigar sun isa ƙauyen ɗauke da muggan makamai da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Lahadi, inda suka dinga bi gida-gida suna sace mutane.

“Duk mutane sun fara guduwa domin ƙauyenmu na daga cikin wuraren da ’yan bindigar suka daɗe suna kai wa hari.

“Daga baya mun gano cewa sun sace sama da mata 50, ciki har da matan aure da ’yan mata,” in ji shi.

Mazaunin ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara da su tura ƙarin sojoji da jami’an tsaro domin yaƙar maharan.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya ci tura domin bai amsa kiran waya ba.