‘Yan bindiga sun sace matar aure da wasu mutum 2 a Jibiya

Da misalin karfe 8:00 na daren Lahadin nan, ranar da kasuwar garin ke ci, ‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane suka shiga cikin garin Jibiya da ke jihar Katsina. Bayan sun shiga, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da matar wani matashin dan kasuwa da ake kira Tasi’u Wali tare da wasu mutum biyu. Har […]

‘Yan bindiga sun sace matar aure da wasu mutum 2 a Jibiya

Da misalin karfe 8:00 na daren Lahadin nan, ranar da kasuwar garin ke ci, ‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane suka shiga cikin garin Jibiya da ke jihar Katsina.

Bayan sun shiga, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da matar wani matashin dan kasuwa da ake kira Tasi’u Wali tare da wasu mutum biyu.

Har zuwa rubuta wannan rahoto babu wanda ya san ta inda suka biyo zuwa gidan da kuma inda suka dosa bayan dauke mutanan. Babu dai rahoton mutuwa ko kawo wani dauki daga jami’an tsaro.

Batun sata da garkuwa da mutane na sake kunno kai a jahar duk kuwa da sasanci da Gwamna Masari ya yi da wadannan mutane da shugabannin su inda har aka yi musayar mutanen da ke hannun kowa ne sashe.