’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano

Maharan sun yi awon gaba da matashiyar bayan karɓar kuɗin fansa a hannun mahaifinta.

’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano

’Yan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta.

Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu.

Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar, kimanin su 10, sun shiga garin da babura ɗauke da muggan makamai.

Sun shiga gidan Alhaji Auwalu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka, sannan suka tafi da kuɗin fansa tare da sacw ‘yarss.

Wani mazaunin garin, Haruna Muhammad, ya ce harin ya jefa al’ummar garin cikin firgici.

Mutane da yawa na zargin cewa wasu mazauna garin ne suka bai wa ’yan bindigar bayanai.

Kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro na ƙoƙarin bin sahun ’yan bindigar da kuma ceto matashiyar.

Ko da yake satar mutane da fashi ba su yawaita a Jihar Kano ba, garuruwa irin su Garo da sauran yankunan Arewacin Kano da ke kusa da jihohin Kaduna da Katsina, sun sha fuskantar hare-haren ’yan bindiga.