’Yan bindiga sun sace manomi da matarsa a gona a Kaduna

Ma’auratan sun je gonar tare da ’ya’yansu uku lokacin da ’yan ta’addan suka kai musu farmaki

’Yan bindiga sun sace manomi da matarsa a gona a Kaduna

’Yan bindiga sun yi garkuwa wani mutum mai suna Bitrus Jayawa tare da matarsa, Misis Martha, a lokacin da suke aiki a gonarsu da ke Katambi, a Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.

Wani mazaunin Katambi, Markus Iliya, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:12 na safe a ranar Litinin, lokacin da ma’auratan ke gyaran gona domin fara shuka, sai kawai ’yan bindigar suka bayyana suka yi awon gaba da su a hannun bindiga.

Ya ce ma’auratan sun je gonar tare da ’ya’yansu uku, inda yaran suka fara hango ’yan bindigar suna shigowa gonar, suka kuma tsere da gaggawa.  “Yaran ne suka fara ganin ’yan bindigar kafin su tsere, sai maharan suka bi ma’auratan suka yi gaba da su,” in ji shi.

Wani jagoran al’umma a yankin, wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ya samu kiran gaggawa, nan take ya sanar da jami’an tsaro da ke Sabon-Kurutu junction. Sai dai kafin sojojin da ke wurin su isa gonar, ’yan bindigar sun riga sun tsere da wadanda aka sace zuwa daji.

Wata majiya ta tsaro daga yankin ta tabbatar da sace ma’auratan, tana mai cewa dakarun sun shiga daji domin bin sawun ’yan bindigar da kuma ceto wadanda aka sace.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Hassan Mansur, bai amsa kira ba har zuwa lokacin da aka kammala rahoton.