’Yan bindiga sun sace mutane 30 a Sallar Asuba a Zamfara
’Yan bindiga sun sace mutane kimanin 30 a masallaci a lokacin Sallar Asuba a garin Tsafe da ke Jihar Zamfara
’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane kimanin 30 a masallaci a lokacin Sallar Asuba a garin Tsafe, hedikwatar Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun mamaye masallacin ne da misalin karfe 5 na Asuba, a lokacin da ake shirin fara salla.
Garba ya ce, “Za mu fara sallar asuba, kwatsam sai ’yan bindiga suka shigo masallaci suka umarci kowa ya fito ya bi su.
“Kowa ya yi kokarin guduwa domin tsira amma suka tare ko’ina suka gargade mu cewa za su kashe duk wanda ya yi yunkurin guduwa.
- Yau za a rufe layukan wayan da ba su da lambar NIN
- An yi wa daliba mai neman shiga jami’a fyade an kashe ta
Shaidan ya bayyana cewa ’yan bindigar sun bar baburansu a nesa da masallacin don kada a lura da motsinsu.
A cewarsa, adadin mutanen da aka sace a masallacin zai iya wuce 30.
Ya kara da cewa “masallacin ya cika a lokacin da suka kai hari kuma kadan ne daga cikin mu suka samu tsira.”
Daya daga cikin shugabannin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bin diddigin ’yan bindigar domin kubutar da wadanda aka sacen.
Karamar hukumar Tsafe dai na daga cikin kananan hukumomin jihar da ke fama da matsalar ’yan bindiga.
Titin Tsafe zuwa Gusau ya zama wuri mafi hadari a jihar inda a kullum ake sace mutane.
A ’yan kwanakin nan an kashe ’yan bindiga da dama a karamar hukumar lokacin da wasu gungun ’yan bindiga guda biyu suka yi arangama.