’Yan bindiga sun sace mutane ana tsaka da cin kasuwa a Taraba

’Yan bindiga sun ritsa jama’a a kasuwar Gongon Maliki da ke ci duk ranar Laraba a Jihar Taraba, suka yi awon gaba da ’yan kasuwa da kayayyakinsu

’Yan bindiga sun sace mutane ana tsaka da cin kasuwa a Taraba

‘Yan bindiga

’Yan bindiga sun ritsa mutane a kasuwar Gongon Maliki da ke ci duk ranar Laraba a Jihar Taraba, suka yi awon gaba da mutane da kayayyaki.

Ana tsaka da cin kasuwar a ranar Larabar nan ’yan bindiga kimanin 50 suka iso a kan babura, suka tare kofar kasuwar suka rika luguden wuta tare da gargaɗin kada wanda ya yi yunkurin ficewa daga kasuwar.

Daga nan suka yi ta tisa keyar ’yan kasuwa tare da kwace musu kudade da kwasar kayan abinci da tufafi da sauransu, suka yi awon gaba da su.

Wakilinmu ya ruwaito cewa da misalin karfe 12.30 na ranar Laraba ne ’yan bindigar suka kai farmaki a kasuwar da ke Karamar Hukumar Yorro ta Jihar Taraba.

Aminiya ta gano cewa ’yan kasuwa da dama da suka zo cin kasuwar daga wasu wurare suna daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.

Wani mazaunin garin mai suna Adamu, ya ce tafiyar maharan ke da wuya jama’a suka watse daga kasuwar, wasu ’yan garin kuma suka yi kaura.

Wakilinmu ya yi kokarin tuntubar kakakin ’yan sandan jihar, amma hakan bai yiwu ba.

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza