’Yan bindiga sun sace mutane, sun kashe wasu 2 a Sakkwato
’Yan bindiga sun sace mutane da dama a kauyen Tsululu kan hanyarsu ta zuwa Sakkwato daga Sabon Birni a Jihar Sakkwato bayan sun harbe direban motar har lahira
’Yan bindiga sun sace mutane da dama a kauyen Tsululu kan hanyarsu ta zuwa Sakkwato daga Sabon Birni a Jihar Sakkwato bayan sun harbe direban motar har lahira.
“Sun kashe mutum ɗaya sun tafi da ɗaya a garin Gatawa bayan sun yi musayar wuta da sojoji tun da safe har dare inda ’yan bindigar suka samu sa’ar kone motar soja daya,” in ji wata majiya.
Ta ci gaba da cewa, “Sojojin ba su yi nasara kan maharan ba, motar sojan ta kafe jami’an suka bar ta suka shiga wata, a nan ne ’yan bindigar suka fito bayan wucewar sojojin suka kone ta a gefen garin Gatawa.
“Haka ma a yau Laraba ’yan bindigar sun tare hanyar Bafarawa zuwa Shanawa a Ƙaramar Hukumar Isa suna karɓar kuɗi a hannun ’yan kasuwar da za su tafi cin kasuwa a ƙaramar hukumar Shinkafi.
- Lakurawa sun tsere bayan sojoji sun ragargaje su a Kebbi
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga
Majiyayar ta ce, “duk wanda aka karɓe kuɗinsa a hakan yake tafiya cin kasuwar ba ya fasawa, don ganin suke gara su tafi kasuwar da su koma gida.”
Ya ce, “’yan bindigar suna cin karensu ba babbaka a yankin, ba tare da wata takura da ake yi masu ba.”
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Jam’in Hulɗa da Jama’a na rundunar sojoji yanki na takwas da na ’yan sanda reshen jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i amma haƙar ba ta cimma ruwa ba.