’Yan bindiga sun sace mutum 150 a ƙauyen Zamfara
Maharan sun kaddamar da hare-haren ne a ƙauyuka hudu da ke yankin
Wasu ’yan bindiga a ranar Juma’a sun sace mutum 150, galibinsu mata da ƙananan yara a Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Maharan sun kuma kashe mutum ɗaya a yankin yayin wani farmaki da ya ɗauki tsawon sa’o’i ana yi.
- Kotu ta kwace kujerun ’yan majalisar Filato na PDP 11, ta ba APC
- Babu hannun Tinubu a shari’ar zaben Kano – Kungiyar Yarabawa
Harin dai na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya bayan ’yan bindigar sun sace mutum 17 a ƙauyen Ruwan Ɗorawa na Ƙaramar Hukumar ta Maru.
Aminiya ta gano cewa maharan dai sun kai farmakin ne a ƙauyukan Mutunji da Kwanar-Dutse da Sabon-Garin Mahuta da kuma Unguwar Kawo.
Wani mazaunin ƙauyen Mutunji, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun kai farmakin ne wajen ƙarfe 9:00 na daren Juma’a, kuma sun kaddamar da hare-haren ne a ƙauyukan huɗu a lokacin ɗaya.
Ya ce, “Suna shiga ƙauyen Mutunji suka fara harbi a sama domin su firgita jama’a. Nan take kuma mutanen suka fara gudun tsira da rayukansu.
“Daga nan ne sai suka shiga kama mutane masu rauni, galibinsu mata da ƙananan yara, saboda duk ƙarfafan garin su tsere.
“Lokacin da suke tsaka da kai harin ne na kira wani abokina a ƙauyen Kwanar Dutse da ke kusa da mu don neman taimako, inda ya shaida min su ma a lokacin harin ake kai musu. Ya ce min lokacin ma yana cikin daji bayan ya tsere da abokansa.
Shi ma wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunan nasa ya ce akwai yiwuwar maharan duka tare suke amma suka raba kansu gida huɗu, kowanne suna kai hari ƙauye ɗaya.
“Mun gano maharan sun ƙaddamar da hare-haren ne a ƙauyukan huɗu a lokaci ɗaya, inda daga bisani suka sake haɗuwa suka yi cikin daji da mutanen da suka kwasa.