’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna

Ana ci gaba da kai mana hare-hare a kai a kai, ana sace mana mutane kusan kullum.

’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna

An sace aƙalla mutum 22 a wasu sabbin hare-hare da ake zargin ’yan bindiga da kaiwa a ƙauyen Kugauta da ke Kusheka da kuma Kitanda da ke Gashere a masarautar Kumana da ke Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin, Emmanuel Johnson, ya bayyana wa Aminiya cewa hare-haren sun afku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren Juma’a.

Ya bayyana cewa ’yan bindigar sun farmaki ƙauyen Kitanda ne da farko inda suka yi awon gaba da mutum 12 —galibinsu mata da ƙananan yara — sannan suka kai hari na biyu a ƙauyen Kugauta inda suka sake sace mutum 10.

Johnson, wanda ya nuna takaicinsa kan yadda rashin tsaro ke ƙara ƙamari a yankunansu, ya ce jami’an ’yan sanda uku ne kacal ke kula da ƙauyen da wasu yankunan da ke makwabtaka da su.

“Ana ci gaba da kai mana hare-hare a kai a kai, ana sace mana mutane kusan kullum,” in ji shi.

“’Yan sanda uku ba za su iya kare mu ba. Ya kamata gwamnati ta tabbatar mana cewa mu ma ’yan Nijeriya ne da ke da ’yancin samun kariya”

Ya ƙara da cewa sama da naira miliyan 60 aka biya a matsayin kuɗin fansa a lokuta daban-daban kuma har yanzu akwai wasu da aka sace da ke hannun ’yan bindigar.

Haka kuma, ya ce hare-haren sun sa mutane da dama ƙauracewa gidajensu.

Johnson ya kuma bayyana yadda matsalolin rashin ababen more rayuwa suka ƙara dagula musu rayuwarsu, musamman rashin kyawawan hanyoyi da asibitoci da kuma makarantu.

Ya ce, “Ba ma iya kai kayan gonarmu kasuwa saboda lalacewar hanyoyin.”

Ya yi kira ga gwamnati da ta tura ƙarin jami’an tsaro, ta kuma kafa ofisoshin ‘yan sanda, tare da na sansanan sojoji a muhimman wurare domin daƙile matsalar tsaron da ke ƙara ta’azzara.

Haka kuma, ya buƙaci sojoji da su kai samamen kawar da sansanonin ’yan bindiga a yankin.

“’Yan bindigar nan sun kassara mana tattalin arzikinmh kuma sun jefa mu cikin talauci. Muna kiran Gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen wannan wahalar da muke ciki,” in ji shi.

Ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ci tura yayin da bai amsa kiran waya da sakonnin da wakilinmu ya tura masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.