’Yan bindiga sun sace mutum 23 a Abuja

Mai unguwar yankin ne ya tabbatar da sace mutanen 23.

’Yan bindiga sun sace mutum 23 a Abuja

ƙofar shiga birnin tarayya Abuja

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 23 a unguwar Dei-Dei da ke Karamar Hukumar Bwari a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Aminiya ta gano cewa an dauke wadanda lamarin ya rutsa da su ne a gidajensu da misalin karfe 9 na dare ranar Litinin.

Mai Unguwar Dei-Dei Ibrahim Galadima yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’an tsaro sun ceto bakwai daga cikin wadanda aka sace.

Amma ya ce jami’an tsaro sun bi sahun ’yan bindigar zuwa daji da nufin ceto ragowar da ke hannunsu.

“Kamar maharan sun fahimci zuwanmu shi ya sa suka saki wasu daga cikin wadanda suka sace,” in ji shi.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu karin haske daga kakakin ‘yan sandan birnin tarayya, Abuja ba.

An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna

Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi

Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data