’Yan bindiga sun sace mutum 30 a Katsina

Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun sace aƙalla mutum 30 da suka haɗa da maza da mata tare da dabbobi masu yawa a Jihar Katsina. BBC ya ruwaito cewa wannan lamari ya faru ne a garin Unguwar Daudu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Funtuwa da tsakar daren ranar Alhamis. Direbobin manyan motoci sun buɗe hanyar […]

’Yan bindiga sun sace mutum 30 a Katsina

Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun sace aƙalla mutum 30 da suka haɗa da maza da mata tare da dabbobi masu yawa a Jihar Katsina.

BBC ya ruwaito cewa wannan lamari ya faru ne a garin Unguwar Daudu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Funtuwa da tsakar daren ranar Alhamis.

Mutane a yankin na cikin zulumi ganin cewa ba su iya zuwa gonaki ɗebo amfanin gonar da suka noma sanadiyar hare-hare da kuma garkuwa da jama’a da ’yan bindigar ke yi domin neman kuɗin fansa.

Bayan abun da ya faru a garin na Unguwar Daudu, a garin Mai ruwa da ke maƙwabtaka da ƙauyen, ’yan bindigar sun yi awon gaba da wasu mutane da suka je ɗebo amfanin gona.

Aminiya ta ruwaito cewa a ƙarshen watan Oktoban da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama wasu mutane 8 da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane da fashi da makami da haɗa baki wajen kisan kai da sauran miyagun laifukan a jihar.