’Yan bindiga sun sace mutum 7 a Abuja

An sace mutanen yayin jama’a suka shiga sallar magariba a masallaci.

’Yan bindiga sun sace mutum 7 a Abuja

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutum bakwai a kauyen Igu da ke yankin Sherefe a Karamar Hukumar Bwari ta babban birnin tarayya.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne da daren ranar Alhamis din da ta gabata.

Wani mazaunin yankin, Muhammad Yahaya, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun isa unguwar ne a lokacin da mutane suka shiga masallaci domin yin sallar magariba.

Yahaya ya ce an yi awon gaba da mutum bakwai, sannan maharan sun harbi mutum daya da bindiga.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan da aka sace wani hakimin yankin, Chebawaza Sariki, amma daga baya aka sako shi a daren Asabar.

Haka kuma, kimanin wata guda, an sace mutum biyu a wasu yankuna biyu na Sherefe.

A baya-bayan nan hare-haren yan bindiga na ci gaba da kamari a wasu yankunan birnin tarayya, Abuja.

Yanzu Yanzu: Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Kano, Haruna Zago ya rasu

NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa

Babban layin wutar lantarki ya faɗi karon farko a 2025

Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda