’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
Al’ummar gari sun yi ƙoƙarin daƙile harin amma suka kasa saboda ƙarancin makamai.
Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin.
Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon gaba da maza biyu da mata shida.
- ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara
- Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai
Wani ɗan uwa ga waɗanda aka sace, Kabiru Usman, ya ce maharan sun zo ne a ƙafa ɗauke da makamai, suka kuma yi garkuwa da matarsa Umma, ɗiyarsa mai shekara 17, da matar ɗan’uwansa da wasu mata biyu daga Tsundu mai makwabtaka.
Ya ce al’ummar garin sun yi ƙoƙarin daƙile harin amma suka kasa saboda ƙarancin makamai, duk da cewa sun sanar da ’yan sanda da sojoji tun kafin faruwar harin bayan samun bayanan cewa ’yan bindigar na dosar yankin.
Ya roƙi gwamnati ta ɗauki mataki wajen ceto mutanen da aka sace da kuma kare rayukan mazauna yankin.
Aminiya ta yi ƙoƙarin ji ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, sai da har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.
Wannan ba shi ne karo na farko da ’yan bindiga suka kai hari Kano ba, don ko a ’yan makonnin da suka gabata, wasu mahara suka afka garin ’Yan Kwada da ke ƙauyen Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono, inda suka yi garkuwa da mata biyar, ciki har da wasu masu shayarwa.