’Yan bindiga sun sace mutum uku a Abuja

A baya-bayan nan dai birnin Abuja na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.

’Yan bindiga sun sace mutum uku a Abuja

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum uku a rukunin gidajen da ke bayan gidajen tsoffin sojoji da ke rukunin gidaje na Kurudu a babban birnin tarayya Abuja.

Rahotonni sun ambato daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin ƙasar, Birgediya Onyema Nwachukwu na tabbatar da faruwar lamarin.

Birgediya Janar Nwachukwu ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Alhamis.

Mazauna rukunin gidajen sun ce maharan sun buɗe wuta a rukunin gidajen kafin daga bisani su arce da mutanen da suka yi garkuwar da su.

Cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels a ƙasar, Birgediya Janar Nwachukwu ya ce dakarun soji sun garzaya rukunin gidajen a lokacin da suka samu kiran gaggawa dangane da abin da ke faruwa.

Ya ƙara da cewa jami’ansu na ci gaba da farautar maharan domin kuɓutar da mutanen.

Shi ma wani mazaunin yankin mai suna John Emmanuel, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:34 na daren Alhamis.

Ya bayyana cewa cikin wadanda aka sacen har da matar wani lauya da surukarsa da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su bayan sun rutsa su da bindiga.

Ya kara da cewa, ’yan bindigar sun riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi a ƙoƙarin su na samun nasarar yin awon gaba da wadanda lamarin ya rutsa da su.

A baya-bayan nan dai birnin Abuja na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, inda ake samun ƙaruwar ayyukan masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025