’Yan bindiga sun sace shugaban kasuwar kayan miya ta Akinyele a Oyo
Maharan sun sace shi bayan idar da sallar Magariba.

Wasu ’yan bindiga sun kai hari Kasuwar Kayan Miya ta Akinyele, kusa da Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, inda suka sace Shugaban Kasuwar, Alhaji Usman Yako.
Bayanan da muka samu daga shugabannin kasuwar sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na dare, jim kadan bayan an idar da sallar Magriba.
- Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa
- Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah
Mataimakin Shugaban Kasuwar, Alhaji Abdul’aziz Abdulwasi’u (Dan Kashi), ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Bayan na koma gida domin shan ruwa, sai yarona ya kira ni ta waya ya shaida min cewa wasu mutane ɗauke da bindigogi sun shigo kasuwa suna harbe-harbe.
“Sun tilasta Shugaban Kasuwa Alhaji Usman Yako ya fito daga motarsa suka kuma tafi da shi a cikin motarsu.”
Shi ma wani ɗan kwamitin kasuwar, Alhaji Abubakar Garba Karaye, ya ce: “Bayan mun idar da sallar Magriba a babban masallacin kasuwa, sai muka ji ƙarar harbe-harbe.
“Lokacin da muka leƙa, sai muka ga wasu mutane suna harbi a kusa da motar Shugaban Kasuwa.
“Bayan sun gama, suka ɗauke shi suka tafi da shi a cikin motarsu, sun bar tasa motar a kasuwa da harbin bindiga a jikinta.”
Shugabannin kasuwar sun ce ba a taɓa samun irin wannan hari tun bayan kafuwar kasuwar shekaru huɗu da suka gabata ba.
Sai dai kafin wanzuwar kasuwar, an yi ta samun rahoton wasu mutane da ake zargi suna ɓoyewa a cikin dazukan da ke kewayen kasuwar.
Har yanzu ba a samu jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ba, domin ba ya ɗaukar waya.