’Yan bindiga sun sace shugaban makaranta da wasu 8 a Kaduna

Maharan sun buɗe wa mutane wuta lokacin da suka kai harin.

’Yan bindiga sun sace shugaban makaranta da wasu 8 a Kaduna

’Yan bindiga sun sace shugaban makarantar sakandaren gwamnati ta Kachia da wasu mutum takwas da ke Jihar Kaduna, a daren ranar Asabar.

’Yan bindigar sun kai harin ne misalin ƙarfe 9:30 na dare, inda suka shiga harbi, wanda hakan ya sa jama’a suka shiga firgici.

Wani mazaunin yankin, Hamza Idris, ya ce mutane sun fara tserewa don ceton rayukansu.

Mazaunan yankin sun ce mutumin farko da aka sace shi ne Ibrahim Tasi’u Imam, wanda shi ne shugaban makarantar sakandare ta gwamnati da ke Kachia Urban.

Sannan malamin addinin Musulunci ne da kuma sakataren ƙungiyar Musulunci ta Fityanul Islam.

Sauran mutanen da aka sace sun haɗa da Alhaji Falalu, matarsa da ’ya’yansa maza guda biyu, sai kuma Alhaji Haladu Hamisu da ’ya’yansa maza guda biyu.

Har wa yau, maharan sun sace wani almajiri.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Mansir Hassan, ya ci tura saboda wayarsa ba ta shiga.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya