’Yan bindiga sun sace uwa da danta a Kaduna

Maharan sun farmaki yankin da misalin karfe 2 na dare.

’Yan bindiga sun sace uwa da danta a Kaduna

Mahara sun yi awon gaba da wata mata da danta a yankin Dogarawa New Layout da ke Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun raunata mutum daya a harin da suka kai da misalin karfe 2 na daren ranar Lahadi, inda suka sace matar auren mai suna Halimatu Sadiya Bello, da danta mai shekara 17 a duniya.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an kwantar da wanda maharan suka yi wa raunin a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika.

Ya kara da cewa maharan kusan su 15 dauke da bindigogi da adduna sun yi wa yankin kawanya, kuma wannan shi ne karo na biyu da suka kai harin a baya-bayan nan.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin kuma sun baza komarsu domin ganin sun kubutar da wadanda aka sacen.

Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi

Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari

Yadda Kano ke samar da madarar Naira biliyan 2.2

An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda