An yi garkuwa da ’yan daukar amarya 55 a Katsina
Akasarin wadanda aka sace kawayen amarya ne daga garin Dandume
’Yan bindiga sun sace mutane 55 a cikin motocin mahalarta daurin aure a garin Damari da ke Karamar Hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina.
Maharan sun far wa ayarin motocin kirar Kanta ne a cikin daren Alhamis, kuma akasarin wadanda aka sace kawayen amarya ne daga garin Dandume.
Wasu rahotanni sun nuna cewa mutum 30 ne aka yi awon gaba da su, saboda ragowar sun samu sun yi tsalle daga motocin marasa rufi.
Sai dai duk da haka mutum uku daga cikin ’yan banga da suka kai dauki a lokacin harin, sun gamu da ajalinsu a musayar wuta da ’yan bindigar.
Shugaban Karamar Hukumar Dandume, Alhaji Basiru Musa, ya tabbatar da harin.
Kananan hukumomin Sabuwa da Dandume na daga cikin waɗanda ’yan bindiga suka fi addaba a Jihar Katsina
Wasu rahotanni sun bayyana cewa a daidai lokacin da aka kai wa masu zuwa daurin auren hari, wasu ’yan bindiga daga Dajin Siddi sun kai farmaki a kauyen Tashar Nadaya, kusa da yankin Gazari a Karamar Hukumar Sabuwa.
A wani harin na daban kuma ’yan bindiga sun harbe wani mutum a kan babur dinsa, suka dauke baburin.
Maharan sun kuma bude wa wasu mutum hudu wuta, suka dauke baburansu.