’Yan bindiga sun sace ’yan gudun hijira a Sakkwato

An kai hare-haren na a ƙauyukan Gasalodi da Tungar Barke da ke ƙaramar Hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato.

’Yan bindiga sun sace ’yan gudun hijira a Sakkwato

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace da yawa daga cikin ’yan gudun hijira  waɗanda suka koma garuruwansu kwanan nan, biyo bayan sabbin hare-hare da aka kai ranar Laraba.

An kai hare-haren na a ƙauyukan Gasalodi da Tungar Barke da ke ƙaramar Hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe, a daidai lokacin da mazauna garuruwan, waɗanda a baya suka fake a maƙwabciyar garin ta Jabo bayan hare-haren farko, inda suke ƙoƙarin sake komawa matsugunansu.

Majiyoyi sun bayyana cewa, maharan sun kuma kora dabbobi da ba a tantance yawansu ba kafin su tsere da mutanen da suka sace.

Wani mazaunin garin Jabo, wanda ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin, ya bayyana cewa mazauna ƙauyen da abin ya shafa sun koma gida kwana ɗaya kacal da ya gabata, bayan sun kwashe makonni da dama a sansanin ’yan gudun hijira.

“Sun koma gida jiya Laraba, amma abin takaici an sace wasu daga cikinsu a safiyar yau. Haka kuma ’yan bindigar sun kwashe musu dabbobi,” in ji majiyar.

Ya ƙara da cewa, tun da farko maharan sun yi barazanar cewa za su dawo idan har mazauna ƙauyen suka yi yunƙurin sake komawa garuruwansu.

“Sun yi wa mazauna kauyen gargaɗin cewa za su dawo da zarar sun koma gida, kuma abin da ya faru ke nan,” in ji shi.

Wani mazaunin garin na daban ya ƙiyasta cewa, an sace kusan mutane 20 a lokacin harin. “Ina gona ta lokacin da na ga mazauna ƙauyen suna gudu da gudu suna komawa Jabo domin tsira daga harin,” in ji shi.

Yayin da wakilinmu ya ziyarci Jabo, ya tarar da yawancin ’yan gudun hijirar suna neman mafaka a makarantun gwamnati, yayin da wasu kuma suka taru a gefen manyan tituna bayan sun tsere daga sabon tashin hankalin.

ɗaya daga cikin matan da suka rasa matsugunansu, Yarmagaji, wata gwauruwa kuma uwar ’ya’ya biyar daga Tungar Barke, ta ce ta kwashe sama da wata guda tana zaune a makaranta bayan an raba su da gidajensu.

“Ina da yara biyar, dukkansu marayu ne. Tun da muka zo nan kusan wata guda da ya gabata, bara nake yi don in ciyar da su saboda ba ni da wata hanyar samun kuɗin shiga,” in ji ta. Ta yi kira ga Karamar Hukumar Tambuwal da sauran hukumomin da suka dace da su samar da kayan agaji ga iyalan da suka rasa matsugunansu.

A Babban Asibitin Jabo, waɗanda suka jikkata sakamakon hare-haren ’yan bindiga na baya-bayan nan sun nuna ɓacin ransu kan abin da suka kwatanta da halin ko-in-kula da gwamnati ke nuna musu. ɗaya daga cikin marasa lafiyar, Abubakar Muhammad, ya bayyana cewa ya sami raunuka da dama na harbin bindiga a hannunsa na hagu a lokacin da aka kai hari a ƙauyen Babban Rafi kimanin makonni uku da suka gabata.