’Yan bindiga sun sace ’yan jarida da iyalansu a Kaduna

’Yan bindigar sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 10:30 na dare suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

’Yan bindiga sun sace ’yan jarida da iyalansu a Kaduna

Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ’yan jarida biyu a ƙauyen Danhonu da ke garin Millennium City na Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Aminiya ta ruwaito cewa gommn ’yan bindigar da suka kai farmaki cikin dare a ranar Asabar sun shiga shiga gidajen ’yan jaridar guda biyu kuma suka yi awon gaba da su da matansu da ’ya’yansu.

Bayanai sun ce ’yan jaridar da abin ya shafa sun haɗa da wakilin jaridar The Nation, Alhaji AbdulGafar Alabelewe, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ’yan jarida ta ƙasa (NUJ), reshen jihar Kaduna da kuma wakilin jaridar Blueprint, AbdulRaheem Aodu.

Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, Taofeeq Olayemi, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Asabar, suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen.

Ya bayyana cewa sun yi awon gaba da Alhaji Alabelewe da matarsa da ’ya’yansu biyu, yayin da suka yi awon gaba da Alhaji Aodu da matarsa sannan suka kyale wata diyarsa da ke fama da rashin lafiya.

Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, amma ba ta samu jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa