’Yan bindiga sun sace ’yan uwan juna 3 tare da gawar mahaifiyarsu a Benuwai

Wasu shaidu sun ce sun ji ƙarar harbe-harbe, lamarin da ya sa suke tsere domin tsira da rayukansu.

’Yan bindiga sun sace ’yan uwan juna 3 tare da gawar mahaifiyarsu a Benuwai

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace wasu ’yan uwan juna uku yayin da suke kan hanyarsu daga Abuja zuwa Jihar Benuwai, domin kai gawar mahaifiyarsu gida don binne ta.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar a kan hanyar Ogobia zuwa Otukpo da ke Ƙaramar Hukumar Ohimini ta Jihar Benuwai.

’Yan uwan na kan hanyarsu na zuwa ƙauyen Iklenyi da ke Ƙaramar Hukumar Okpokwu, inda za a binne mahaifiyarsu wadda ta rasu a Abuja, lokacin da aka yi garkuwa da su.

Mazauna yankin sun ce sun ji ƙarar harbe-harbe tsakanin karfe 3 na dare zuwa 4 na safe, lamarin da ya sa mutane da dama suka tsere domin neman tsira da rayukansu.

Shaidu sun ce motar da ’yan gida ɗayan ke tafiya da ita ta samu matsala a kan hanya, wanda ya sa suka maƙale har kusan karfe 2 na dare.

Bayan an gyara motar jim kaɗan da tashinsu suka suka ci karo da mahara.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Ohimini, Gabriel Adole, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa yana kan hanyarsa ta zuwa waje  domin gano ainihin abin da ya faru.

Ya ce, “Eh, ina kan hanyata zuwa wajen domin tabbatar da abin da ya faru.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Benuwai, ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Hakazalika, kakakinta, DSP Udeme Edet, ba ta amsa kiran waya ko saƙon kar-ta-kwana da aka aike mata ba.