’Yan bindiga sun sake kashe mutun 7 a Nasarawa
Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura ya yi Allah wadai da wani mummunan hari da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su ba suka kai wasu kauyukan Tibabe da ke kewayen garin Kadarko da ke yankin karamar Hukumar Keana a daren ranar Litinin da ta gabata, inda suka kashe mutum 7, dukansu ’yan […]

Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura ya yi Allah wadai da wani mummunan hari da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su ba suka kai wasu kauyukan Tibabe da ke kewayen garin Kadarko da ke yankin karamar Hukumar Keana a daren ranar Litinin da ta gabata, inda suka kashe mutum 7, dukansu ’yan kabilar Tibi.
Gwamnan, wanda ya ziyarci garin a Talatar da ta gabata don jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon harin, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi duka mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaro a yankin baki daya, don kauce wa sake aukuwar lamarin a yankin nan gaba. A cewarsa, gwamnati za ta turo isassun jami’an tsaro ciki har da sojoji, wadanda za su rika sintiri a kasa da sama, ta amfani da helikwafta don tabbatar da tsaro tare da kame wadanda suke aikata irin wadannan munanan ayyuka a yankin.
Gwamnan ya kuma bukaci al’ummar yankin su zauna lafiya da junansu, su kuma daina guduwa daga kauyukansu zuwa cikin gari, domin a cewarsa hakan zai kara jawo tsoro da tada hankalin al’umma. Ya shawarce su da kada su tafi gonakinsu a yanzu, sai kura ta lafa don kare kansu. Ya kara da cewa bayan jami’an tsaro, gwamnati za ta kuma tallafa wa wadanda a yanzu haka suke gudun hijira a makarantun firamaren gwamnatin jihar da ke garin Kadarko cikin gaggawa don saukake musu wannan bala’i da ya same su.
Wakilinmu ya gano cewa a halin yanzu al’ummomin kauyukan da ke kewayen garin Kadarko da suka hada da Giza da Ngur-Giza da Gidan-Sule da Sarkin-noma da sauransu duk sun gudu sun bar gidajensu, sakamakon aukuwar lamarin suna zaman hijira a makarantun firamaren, yayin da wasu suna barin karamar hukumar baki daya zuwa wasu garuruwa daban.