’Yan bindiga sun sake kashe ’yan sanda 2 a Imo

Maharan sun yi wa ’yan sandan kwanton bauna.

’Yan bindiga sun sake kashe ’yan sanda 2 a Imo

Wasu ‘yan sanda a bakin aiki

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu a mahadar Ngor Okpala da ke karamar hukumar Ngor Okpala a Jihar Imo.

’Yan bindigar da ake zargin ’yan kungiyar ’yan awaren Biyafara ne (IPOB), sun kai farmaki ga ‘yan sandan da ke aiki a wani shingen binciken ababen hawa a yankin.

Biyu daga cikin ma’aikatan da aka ce suna aiki ne a sashen yaki da ta’addanci (CTU) an kashe su nan take, yayin da ’yan ta’addan suka gudu.

Wannan na zuwa bayan da aka kashe ’yan sanda biyar a yankin.

Kazalika a watan Maris, wasu ’yan bindiga sun yi wa jami’an tsaron Sibil Difens kwanton guda biyar bauna, inda suka kashe su a yankin.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Henry Okoye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, ya ce ’yan sandan sun yi musayar wuta da maharan.

Ya ce, “Eh, zan iya tabbatar da mutuwar jami’anmu guda biyu na sashen yaki da ta’addanci, wasu ’yan bindiga ne da ke da alaka da IPOB.

“Yaranmu sun yi artabu mai tsanani da maharan, wadanda suka gudu cikin jeji suka bar motarsu, wadda muka kwato ya sa muka gano kayan laifi a ciki.

“Don haka a yanzu, muna gudanar da wani samame a Ngor Okpala domin kama su tun da mun yi imanin cewa sun tsere da munanan raunukan harbin bindiga.

“Muna kira ga cibiyoyin kiwon lafiya da su sanya ido tare da kai rahoton duk wanda ya je neman magani da harbin bindiga,” in ji kakakin.