’Yan bindiga sun sake sace mutum 46 a Zamfara

Hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da kawo koma baya ga harkokin noma da kasuwanci a yankin.

’Yan bindiga sun sake sace mutum 46 a Zamfara

’Yan bindiga sun sace mutum 46 a wani hari da suka kai garin Gana da ke Jihar Zamfara.

Harin ya ƙara nuna yadda matsalar tsaro ke ta’azzara a yankin, duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kare al’umma.

Bayanai na cewa ɗan bindigar daji, Dogo Giɗe, ya sanya wasu garuruwa 23 da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe cikin Jihar a Zamfara, da su biya harajin Naira miliyan 100 ko su ci gaba da fuskantar hare-hare.

Sai dai, mazauna yankin sun musanta cewa akwai barazana mai kama da wannan.

A makon da ya gabata, ’yan bindiga sun kai hari garin Gana, inda suka buɗe wa jama’a wuta, sannan suka ƙone gidaje da wuraren sana’a, sannan suka sace mutane, ciki har da mata da yara.

Wannan hari yana daga cikin jerin hare-haren da aka yi a wannan jihar a cikin ’yan kwanakin da suka gabata.

Jami’an tsaro sun ce sun kama wasu daga cikin jiga-jigan ’yan bindiga a jihar, inda suke ci gaba da bincike don kama sauran.

Matsalar tsaro a yankin Arewa Maso Yamma na kawo naƙaso ga harkokin noma da kasuwanci, wanda ke ƙara jefa al’umma cikin talauci.