’Yan bindiga sun saki bidiyon Janar Rabe da matarsa a hannunsu

A cikin bidiyon an ga Janar Rabe da matarsa a tsaye suna bayyana bukatun masu garkuwar

’Yan bindiga sun saki bidiyon Janar Rabe da matarsa a hannunsu

Masu garkuwar tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Runundar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo-Janar Abubakar Rabe (mai ritaya), sun saki bidiyo da ke nuna ma’auratan a hannunsu.

’Yan ta’addan sun saki bidiyon ne kwana bakwai kacal bayan sace Manjo-Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) tare da matarsa a kan hanyar Karaduwa–Matazu da ke Jihar Katsina.

Bidiyon mai tsawon minti hudu, wanda ya yadu a shafukan sada zumunta, ya nuna ma’auratan tsaye suna bayyana bukatun masu garkuwar.

A jawabinta, matar Janar Rabe ta bayyana cewa ’yan bindigar suna bukatar a saki wasu mutane uku da aka kama, masu suna Sani, Aminu da Nasiru. Ta ce biyu daga cikin mutanen an kama su ne a Jikamshi, Jihar Katsina, na ukun kuma aka kama shi a Kano.

Ta ce haka kuma, ’yan bindigar suna neman a mayar musu da dabbobin da aka kwace daga hannunsu.

Ta roki Gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin kananan hukumomi biyar su taimaka wajen cika wadannan bukatu domin a sako su.

A bayaninsa da ya yi, Janar Rabe ya bukaci a yi kokari wajen tabbatar da zaman lafiya, yana mai cewa masu garkuwar sun nuna sha’awar tattaunawa da zaman lafiya.

Aminiya ta lura cewa a cikin bidiyon babu maganar kudin fansa. Haka kuma, an ga ma’auratan cikin natsuwa da tsabta, abin da ke nuna alamar ba a azabtar da su ba.

Zuwa yanzu dai babu wata wata sanarwa da Gwamnatin Jihar Katsina ko hukumomin tsaro game da bidiyon da masu garkuwar suka saki.