’Yan bindiga sun saki malamin da suka sace a Zariya

Ragowar waɗanda ’yan bindigar suka ’yantar sun haɗa da ƙanin malamin, Sidi Aliyu Sahabi.

’Yan bindiga sun saki malamin da suka sace a Zariya

Malam Ismaila Sahabi

Malamin nan na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya da ’yan bindiga suka sace, Malam Isma’ila Sahabi, ya shaƙi iskar ’yanci.

’Yan bindigar sun saki Malam Isma’ila Sahabi da wasu mutum biyu bayan kwashe kwanaki 31 a hannunsu.

Ragowar waɗanda ’yan bindigar suka ’yantar sun haɗa da ƙanin malamin, Sidi Aliyu Sahabi da kuma wani mutum ɗaya wanda aka ɗauke su tare.

Tun farko dai an samu wani mutum ɗaya da ya tsere daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Aminiya ta gano cewa mafi waɗanda ’yan bindigar suka yi garkuwa da su mazauna unguwar Tudun Wada ta Zariya ne waɗanda kuma suke da gonaki a Kasuwar Magani da ke Ƙaramar Hukumar Chikun, inda suke zuwa domin gudanar da aikin noma.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, jama’ar Tudun Wada na cike da farin cikin sakin waɗannan mutane bayan sun duƙufa da addu’oi.

Ƙoƙarin da Aminiya ta yi domin gano ko an biya maharan kuɗin fansa gabanin sakin waɗanda lamarin ya shafa ya ci tura.