’Yan bindiga sun sare kan matashi a Filato
’Yan bindiga sun fille kan wani matashi mai shekara 30 a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Gwamnan Filato Caleb Muftwang
’Yan bindiga sun fille kan wani matashi mai shekara 30, Elisha Abbas Saku, a kauyen Riwhie-Chwo da ke Nzharuvo, Miango, a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Jaridar Punch ta ruwaito mazauna yankin na cewa ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis da misalin karfe 10 na dare, lokacin da ’yan bindigar suka shigo cikin al’umma, abin da ya jefa jama’a cikin firgici da ruɗani.
Ƙungiyar Matasan Irigwe ta tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, inda ta bayyana kisan a matsayin mummunan ta’addanci.
Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ƙungiyar, Joseph Yonkpa, wanda ya sanya hannu kan sanarwar, ya yi addu’a ga Allah Ya jiƙan mamacin tare da neman ta’aziyya ga al’ummar Irigwe baki ɗaya.
- Tsagin Wike na PDP zai tsayar da ɗan takarar da zai ƙalubalanci Tinubu
- Ƙungiyoyin PDP 293 sun koma APC a Yobe
Sanarwar ta ce: “A daren jiya, 16 ga Afrilu, 2026, ’yan bindiga sun yi wa Elisha Abbas Saku, mai shekara 30, kwanton bauna tare da yanke kansa a Riwhie-Chwo, Nzharuvo, Miango, Ƙaramar Hukumar Bassa, Jihar Filato.”
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Alabo Alfred, bai samu a waya ba lokacin da aka nemi jin ta bakinsa kan lamarin.
Wannan hari ya ƙara jaddada matsalar tsaro da ke ta faruwa a wasu sassan Jihar Filato, musamman a Bassa, inda al’umman manoma ke yawan fuskantar hare-hare.