’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 23 a sansanin sojoji
Aƙalla ƙauyuka 23 ne ’yan bindiga suka tarwatsa a ƙauyukan da cikin sansanin horon sojojin atilare da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora a Jihar Neja.
Aƙalla ƙauyuka 23 ne ’yan bindiga suka tarwatsa a ƙauyukan da cikin sansanin horon sojojin atilare da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora a Jihar Neja.
Barikin Sojoji da ke Kontagora babban sansanin soji ne da ke horar da mayaƙan rundunar atilare.
Al’ummomin da ’yan bindiga suka tarwatsa suna cikin filin wannan rundunae soji ne a ƙaramar hukumar.
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Neja mai wakiltar Kontagora II, Abdullahi Isah, ya shaida wa majalisar a ranar Talata cewa sansanin horon sojojin ya ratsa ƙananan hukumomin Kontagora da Mariga.
- Yadda ’yan ta’adda suka addabi babban layin lantarkin Arewa.
- DAGA LARABA: Adawar Gwamnonin Arewa da Ƙudurin Haraji: Kishin Ƙasa Ko Son Zuciya?
Ya ce amma yawan hare-haren ’yan ta’adda ya sa al’ummar yankin kaurace wa gidajensu.
“’Yan fashin daji sun kafa sansanoni aƙalla guda shida a dajin, wanda yanzu ya zama maɓoyarsu, inda suke barazana ga al’ummar ƙananan hukumomin Kontagora da Mariga”, in ji shi.
Isah ya bayyana cewa mutanen yankin da dama suna hannun ’yan bindiga da suka yi garkuwa da su kuma har yanzu ba a sako su ba.
Don haka majalisar ta buƙaci gwamnatin jihar ta tattauna da hukumomin soji domin su ƙara ƙaimi wajen fatattakar ’yan fashin dajin daga yakin domin mutane su samu damar komawa gidajensu.
Babban Barikin Sojoji da ke Kontagora babban sansanin soji ne da ke matsayin cibiyar horar da mayaƙan atilare.