‘Yan bindiga sun tarwatsa mutum dubu 16 a Benuwe
Harin ‘yan bindiga ya tarwatsa mutanen karkara a jihar Benuwe wanda hakan ya sa dalibai dubu 20 suka bar makarantu yayin da mutum dubu 16 suka bar muhallansu suka koma sansanin ‘yan gudun hijira a jihar. Shugaban hukumar ilimin bai daya Philip Tachin ne bayyana wa manema labarai hakan a Makurdi babban birnin jihar Benuwe. […]
Harin ‘yan bindiga ya tarwatsa mutanen karkara a jihar Benuwe wanda hakan ya sa dalibai dubu 20 suka bar makarantu yayin da mutum dubu 16 suka bar muhallansu suka koma sansanin ‘yan gudun hijira a jihar.
Shugaban hukumar ilimin bai daya Philip Tachin ne bayyana wa manema labarai hakan a Makurdi babban birnin jihar Benuwe. Ya kuma ce a yanzu an lalata makarantun firamare na gwamnati sama da 50.