’Yan bindiga sun tarwatsa zaman majalisar Libya

’Yan bindiga sun fada cikin zauren Majalisar Dokokin kasar Libya inda suka tarwatsa zaman majalisar a daidai lokacin da wakilanta ke kokarin zabar sabon Firayi Ministan kasar a shekaranjiya Laraba, kamar yadda jami’an gwamnatin kasar suka ce.Manema labarai sun ce ’yan majalisar sun sulale daga ginin maja-lisar bayan da suka ji karar harbe-harben bindiga.’Yan majalisar […]

’Yan bindiga sun tarwatsa zaman majalisar Libya
’Yan bindiga sun tarwatsa zaman majalisar Libya

’Yan bindiga sun fada cikin zauren Majalisar Dokokin kasar Libya inda suka tarwatsa zaman majalisar a daidai lokacin da wakilanta ke kokarin zabar sabon Firayi Ministan kasar a shekaranjiya Laraba, kamar yadda jami’an gwamnatin kasar suka ce.
Manema labarai sun ce ’yan majalisar sun sulale daga ginin maja-lisar bayan da suka ji karar harbe-harben bindiga.
’Yan majalisar na kokarin zaben ne bayan da Abdullah al-Thinni, ya yi murabus daga mukaminsa na Firayi Ministan a farkon wannan wata saboda harin da masu dauke da mukamai suka kai masa shi da iyalansa.
kasar Libya ta fada cikin rikici ne bayan da kungoyoyin masu dauke da makamai suka kifar da gwamnatin marigayi Shugaba Mu’ammar Gaddafi a shekarar 2011.
A cewar gidan rediyon BBC Landan ba a tabbatar da rahoton farko da ke nuna cewa mutane da dama sun samu raunuka a harin na ranar Talata ba. Kuma ba a gano ko su wane ne suka haddasa wannan tashin hankali ba.
An rika kai hari ga majalisar dokokin Libya a shekara daya da rabi da suka gabata.
Kuma ’yan majalisar sun kasa samun matsaya kan nada sabon Firayi Ministan a lokacin da aka kai harin. Sun dai yi zagaye na farko na zaben inda suka zabi mutum biyu daga cikin ’yan takara bakwai, inda aka dage zagaye na biyu. Kuma kafofin labarai na kasar sun ce za a gudanar da zaben a ranar Lahadi mai zuwa.