’Yan bindiga sun tilasta min binne ’ya’yana 3 a daji

Aisha ta ce, an yi garkuwa da ita tare da ’ya’yanta yayin wata tafiya, inda suka shafe watanni shida da kwanaki biyar a hannun masu garkuwa da mutane.

’Yan bindiga sun tilasta min binne ’ya’yana 3 a daji

Wata mata mai suna Aisha ta bayyana irin azabar da ta sha a hannun ’yan bindiga a Jihar Zamfara, inda ta ce an tilasta mata binne ’ya’yanta uku bayan sun rasu a lokacin da suke tsare a daji.

Aisha ta ce, an yi garkuwa da ita tare da ’ya’yanta yayin wata tafiya, inda suka shafe watanni shida da kwanaki biyar a hannun masu garkuwa da mutane.

Ta ce, ta fuskanci yunwa, ƙishirwa da rashin lafiya, tare da rasa dukkan ’ya’yanta a lokacin da suke tsare.

A cewarta, bayan rasuwar ’ya’yan nata, ’yan bindigar sun umarce ta da ta binne su da kanta.

Aisha ta ce daga bisani ta samu damar tserewa cikin dare, inda ta shafe kwanaki uku tana neman hanyar fita daga dajin kafin ta isa wani gari.

Yanzu haka ta yi kira ga masu hannu da shuni da hukumomi da su taimaka mata da magani da abinci domin farfaɗowa daga halin da ta shiga.