’Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake a Imo

An dai sace shi ne a fadarsa, wajen misalin karfe 2:30 na daren Alhamis.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake a Imo

’Yan bindiga

Wasu ’yan bindiga da yawansu ya kai kusan 10 sun mamaye masarautar Mbutu da ke Karamar Hukumar Aboh Mbaise ta Jihar Imo, inda suka yi awon gaba da basarakenta, Eze Damian Nwaigwe.

An dai sace shi ne a fadarsa, wajen misalin karfe 2:30 na daren ranar Alhamis, kamar yadda wata majiya a yankin da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu.

A cewar majiyar, “An sace basaraken masarautar Mbutu da ke Karamar Hukumar Aboh Mbaise ta Jihar Imo, Eze Damian Nwaigwe, da sanyin safiyar nan.

“’Yan bindigar da suka zo suka tafi da shi suna da yawa sosai.

“Sun zo ne a kan mota, kuma sun kai su 10, sannan suka yi wa fadarsa kawanya, suka yi ta harbi a iska, kafin daga bisani su wuce da shi a cikin motar,” inji majiyar.

Rahotanni dai sun ce fadar dai ba a tsakiyar gari take ba, lamarin da ya sa mutane ba su iya zuwa don kawo dauki ba.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar, CSP  Mike Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma ce tuni rundunar ta bazama wajen ganin ta ceto basaraken ba tare da an cutar da shi ba.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya