’Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai 287 a Kaduna

Yaran da lamarin ya rusta da su shekarunsu sun kama ne daga takwas zuwa 15.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai 287 a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani. (Hoto: Gwamnatin Jihar Kaduna).

’Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban firamare da na sakandare 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Aminiya ta ruwaito yadda lamarin ya faru a safiyar ranar Alhamis amma babu haƙiƙanin adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Sai dai wani malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi wanda ya tsallake rijiya da baya ya bayyana cewa ɗalibai 287 ne aka sace a makarantar.

Malamin makarantar ya ce ’yan bindigar sun kashe mutum daya sannan yaran da lamarin ya rusta da su shekarunsu sun kama ne daga takwas zuwa 15.

Sani Abdullahi ya ce, “a bangaren sakandare ɗalibai 187 ne suka bace amma bangaren firamare ɗalibai 125 da farko ba a gansu ba amma daga bisani guda 25 sun dawo.”

Malamin ya bayyana cewa “na shigo makaranta misalin karfe 7:45 sai na shiga ofishin firinsifal kuma sai ya ce min in waiga baya, ina juyawa sai naga ’yan bindiga sun kewaye makarantar.

“Saboda haka muka ruɗe muka rasa inda za mu shiga

“Sai ’yan bindigar suka ce mu shiga daji, kuma muka yi musu biyayya domin suna da yawa kuma ɗaliban kusan 700, suna biye da mu.

“Don haka, lokacin da muka shiga daji, na yi sa’a na tsere tare da wasu da yawa.

“Na koma ƙauyen na ba da labarin abin da ya faru ga al’umma. Don haka nan take ‘yan banga da jami’an hukumar KADVIS suka bi ‘yan ta’addan, amma ‘yan banga ba su yi nasara ba, hasali ma ”yan bindigar sun kashe daya daga cikin ‘yan banga, mun binne shi ba da jimawa ba.

Ya bayyana cewa ana cikin wani hali na fargaba tun bayan sace daliban a safiyar Alhamis.

Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce “Babu wani gida a Kuriga wanda wannan abin bai shafe shi ba.”

Bayanai sun ce abin ya faru ne a lokacin da yaran suke halartar taro na asambili, kana daga bisani ’yan bindigar su kora ɗaliban da suka sace ɗin cikin daji.

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani wanda ya ziyarci makarantar bayan faruwar lamarin, ya bayyana cewa bai ga ta zama ba har sai an kubutar da yaran gaba ɗayansu.

“A matsayina na Gwamnan da kuka zaɓa, ina tabbatar muku da cewa da yardar Allah dukkan yaran za su dawo ba tare da wani abu ya same su ba.

“Kafin na ƙaraso nan, na yi magana da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na kasa, Malam Nuhu Ribadu.

“Za mu ci gaba ƙoƙari saboda jami’an tsaro sun ɗauki harama da zage damtse kuma da yardar Allah za mu kubutar da yaran.

“Tunda na ji labarin bakin ciki na faruwar wannan al’amari ban samu natsuwa ba domin duk wani yaro a Jihar Kaduna yarona ne. Don haka, ba na son ku mutane ku sa damuwa a ranku.

“Mu ci gaba addu’ar Allah Ya taimake mu, kuma a namu bangaren gwamnati ba za mu huta ba har sai yaran nan sun dawo gida.

“Za mu zaɓi mutane bakwai daga cikin wannan al’umma, waɗanda za su kasance cikin kwamitin tattaunawa,” a cewar gwamnan.

Zaɓen Edo: An fara ƙirga ƙuri’u

Zaɓen Edo: INEC ta tsawaita kaɗa ƙuri’a a wasu yankuna

’Yan sanda sun kama mai yi wa ’yan bindiga safarar makamai a Kaduna

Gwamnan Kano ya raba wa makarantu kujeru da tebura 73,000