’Yan bindiga sun sace basarake da matarsa
’Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake da matarsa a cikin ruwan sama.
Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani basarake da matarsa a zuwa inda ba a sani ba.
Ana cikin ruwan sama da dare ne ’yan bindiga suka kutsa gidan basaraken a kauyen Araro da ke Karamar Hukumar Ido ta Jihar Oyo suka yi gaba da shi.
Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Oyo, Adewala Osifeso ya ce “Ana kokarin kubtuar da su tare da kama wadanda suka sace sun.”
Wani mazaunin kauyen ya ce ’yan bindigar sun dauke basaraken tare da matarsa ne da misalin karfe tara da dare ranar Talata.
Wakilinmu ya gano cewa maharan sun far wa kauyen ne a yayin da ake ruwan sama, suka wuce kai tsaye zuwa gidan basaraken.